Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti{a.s} - ABNA- Ibrahim Ra’isi ya bayyana hakan nea yammacin jiya a lokacin da yake ganawa da shugaban majalisar tsaron kasa na kasar Hadaddiyar Daular Larabawa Tahnun Bin Zayed a ziyarar da ya kai birnin Tehran.
Ra’isi ya ci gaba da cewa, siyasar gwamnatinsa ita ce karfafa alaka tsakanin Iran da dukkanin kasashe makwabta, musamman ma kasashen yankin tekun Fasha, wadanda suke da tsohuwar alaka ta tarihi a tsakaninsu.
Haka nan kuma ya bayyana cewa Hadaddiyar Daular Larabawa da Iran kasashe masu matukar muhimamnci a yankin gabas ta tsakiya, baya ga haka kuma kasar daya ce daga cikin kasashe masu makwabtaka da Iran, wanda ya zama wajibi ga kasashen biyu su yi aiki tare dukkanin bangarori domin amfanin al’ummominsu.
A nasa bangaren shugaban majalisar tsaron kasa na kasar Hadaddiyar Daular Larabawa Tahnun Bin Zayed ya bayyana cewa, kasarsa za ta bude wani sabon shafin alaka ta musamman tare da kasar Iran, kuma wannan zai kara tabbata ne a ziyarar da ake sa ran shugaba Ra’isi zai kai kasar ta Hadaddiyar daular Larabawa a nan gaba.
342/